Matthew 20

Misali na Maʼaikata a Gonar Inabi

1“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yǎ yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. 2Ya yarda yǎ biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.

3“Wajen saʼa ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. 4Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ 5Saboda haka suka tafi.

“Ya sāke fita a saʼa ta shida da kuma saʼa ta tara, ya sāke yin haka.
6Wajen saʼa ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’

7“Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’

“Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’

8“Saʼad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira maʼaikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara da waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’

9“Maʼaikatan da ka ɗauka wajen saʼa ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. 10Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. 11Saʼad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. 12Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin saʼa ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’

13“Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? 14Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’

16“Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”

Yesu Ya Sāke Yin Zancen Mutuwarsa

17To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu, 18“Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa 19za su kuma bashe shi ga Alʼummai su yi masa baʼa, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”

Roƙo na Mahaifiya

20Sai mahaifiyar ʼyaʼyan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ʼyaʼyanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yǎ yi mata wani abu.

21Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?”

Ta ce, “Ka sa daga cikin ʼyaʼyan nan nawa biyu, ɗaya yǎ zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”

22Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”

Suka amsa, “Za mu iya.”

23Yesu ya ce musu, “Hakika za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”

24Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ʼyanʼuwan nan biyu. 25Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. 26Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yǎ zama bawanku, 27kuma duk mai son zama shugaba, dole yǎ zama bawanku, 28kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yǎ yi bauta, yǎ kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Makafi Biyu Sun Sami Ganin Gari

29Saʼad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

31Mutane suka tsauta musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

32Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”

33Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”

34Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.

Copyright information for HauSRK